Kyautukan da Tinubu ya bai wa tawagar Super Eagles
13 Fabrairu 2024
Tawagar Super Eagles da ta wakilci Najeriya a gasar cin kofin ƙwallon ƙafa ta nahiyar Afirka ta koma gida. Bayan komawarta shugaban ƙasar, Bola Ahmed Tinubu ya karɓi baƙuncin su a fadarsa da ke Abuja.
Ƴan wasan na Super Eagles da masu horas da su sun isa gida ne a daidai lokacin da suke shan yabo da kuma suka a lokaci guda.
Masoya ƙwallon ƙafa a Najeriya sun so ganin ƙasar ta samu nasarar lashe kofin a karo na huɗu, sai dai hakan bai cimma nasara ba.
Mai masaukin baƙi Ivory Coast ce ta yi wa Najeriya kancal a wannan buri nata, inda aka doke Super Eagles ɗin da ci biyu da ɗaya.
Duk da cewa ba su samu nasara ba a wasan na ƙarshe, tun farko shugaban na Najeriya ya yaba wa rawar da suka taka, sannan kuma bayan isar su gida shugaban ya tarbe su inda ya yi musu ruwan kyaututtuka, waɗanda suka haɗa da:
Lambar karramawa ta ƙasa (MON)
Farkon abin da shugaban ƙasar ya yi shi ne karrama ilahirin tawagar da lambar yabo ta 'Member of the Order of the Niger', wato MON.
Wannan lamba ita ce ta farko a cikin matakan lambar yabo ta ƙasa ta Najeriya.
Ana bayar da irin wannan lambar yabo ne domin karrama wasu mutane da suka gudanar da wani aiki wanda ya zamo mai alfanu ga ƙasar baki ɗaya.
Kyautar fili
Shugaban na Najeriya ya kuma sanar da bayar da kyautar fili ga dukkanin ƴan wasan a birnin tarayya, Abuja.
Nan take Ministan Birnin Tarayya, Nyeson Wike ya raba wa tawagar ta Super Eagles takardun mallakar filaye.
Kyautar gida
Kyauta ta uku da shugaban ya sanar ga tawagar ta Super Eagles ita ce kyautar gida, sai dai ba a bayyana inda gidan zai kasance ba.
Za mu ci kofi a gasa mai zuwa - Ekong
A lokacin da ya yi jawabi a madadin ƴan wasan na Super Eagles, mataimakin jagoran ƴanwasan William Troost Ekong ya ce za su ƙara ƙaimi a gasa ta gaba domin ciyo kofin.
Ya ce "Mun yi murna da goyon bayan da kuka nuna mana a gasar da aka yi a Ivory Coast. Mun yi iyakar bakin ƙoƙarinmu. Na so a ce yanzu mun kawo maka kofin ne."
"A 2019 na zo nan da kyautar tagulla. Yanzu ga shi mun zo da lambar azurfa. Mun yi alƙawarin za mu ci gaba da ƙara ƙaimi, dawowar mu ta gaba za mu zo ne da zinare."
ncG1vNJzZmivp6x7o67CZ5qopV%2Bdrra%2FwGiYq6yZmLmmv46com5unGi7qLGYa6Y%3D